4 Mayu 2020 - 03:41
Noam Cheomsky: Takunkuman Amurka Kan Iran A Yanayi Na Corona Halin Keta Ne

Masalin harsuna da kuma falsafa dan kasar Amurka, Noam Cheomsky wanda ya bayyana hakan, ya kuma kara da cewa; Cutar da Donlad Trump yake fama da ita, ita ce ta takurawa da cutar wasu.

(ABNA24.com) Masalin harsuna da kuma falsafa dan kasar Amurka, Noam Cheomsky wanda ya bayyana hakan, ya kuma kara da cewa; Cutar da Donlad Trump yake fama da ita, ita ce ta takurawa da cutar wasu.

Cheomsky ya soki gwamnatin ta Amurka da kakkausar murya akan yadda ta ke ci gaba da matsin lamba mai tsanani akan al’ummar Iran a lokacin da ake fama da matsalar corona. Masanin dan kasar Amurka ya kuma kara da cewa ci gaba da aiki da takunkumin ba halartacce ba ne.

Noam Cheomsky wanda kamfanin dillancin labarai na; Irna” ya yi hira da shi ya kuma ce, takunkumin na Amurka ya taimaka wajen karuwar cutar ta corona.

Ha ila yau, Cheomsky ya yi kira da a kawo karshen takunkumin na Amurka.

Dangane da siyasar cikin gidan Amurka, masanin ya kuma yi gargadin cewa; sake zabar Donald Trump a matsayin shugaban kasar Amurka yana tattare da matsala ga ita kanta Amurkan da kuma duniya baki daya.


/129